Dakarun rundunar sojin Najeriya sun tarwatsa wata maboyar mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutane a dajin Edimogbo da ke ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu a Jihar Kogi, tare da kwato harsasai 1,000 da wasu kayayyaki.

Sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar sojin, Kanal Appolonia Anele, ta fitar ranar 2 ga Nuwamba, 2026, ta ce dakarun bataliya ta 21 ta kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan mutanen da ake zargi da fakewa a dajin.

Rundunar ta ce lokacin da dakarun suka nufi maboyar, waɗanda ake zargin sun harba bindiga domin sanar da sauran ’yan ƙungiyarsu, kafin su tsere zuwa cikin dajin. Sojojin sun bi bayansu, amma ba su yi artabu da su ba.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai harsasai 1,000 kirar 7.62mm x 54, bindiga guda bakwai, shebur biyu, famfon hannu guda ɗaya, wayar salula, na’urar Glo ta intanet da kuma kwalbar mai. An kuma samu sabulu, tufafi, takalma da babura shida kirar Daylong.

Sanarwar ta ce ana ci gaba da bincike a yankin domin gano inda waɗanda suka tsere suka fake da kuma cafke su.

Rundunar sojin ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifuka, musamman masu garkuwa da mutane, tare da kira ga jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *