Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta gudanar da taron tattaunawa da ƙungiyoyin matasa kan rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zaɓe a babban zaɓen 2027.

Taron ya gudana ne a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, a Police Officers’ Mess da ke Bompai, Kano, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar YOSPIS da gidauniyar Aminu Magashi Garba Foundation.

Taron mai taken “Matasa, Zaman Lafiya da Sahihin Zaɓen 2027” ya samu halartar ɗalibai, ƙungiyoyin mata, matasa lauyoyi, jami’an ’yan sanda, ’yan ƙwallon ƙafa, masu tasiri a kafafen sada zumunta, ’yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula.

A cikin jawabinsa, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce matasa sun fi kashi 60 cikin 100 na masu kaɗa ƙuri’a, kuma suna taka muhimmiyar rawa a harkokin zaɓe, sai dai ya yi gargaɗin cewa bai kamata a sake amfani da su wajen tada hankalin jama’a, yaɗa kalaman ƙiyayya da labaran ƙarya ba kamar yadda aka sha gani a wasu lokuta.

Bakori ya bayyana cewa rundunar, ta hannun kwamitin haɗin gwiwar hukumomin tsaro kan zaɓe (ICCES), ta fara gano wuraren da ka iya fuskantar rikici a ƙananan hukumomi 44 na jihar, tare da shirya horas da jami’an tsaro da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan al’umma.

Ya kuma yi gargaɗin cewa za a ɗauki matakin da ya dace da doka kan duk wanda ya yi ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiya, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

A nata jawabin, Daraktar YOSPIS, Zainab Nasir Ahmad, ta buƙaci matasa da su guje wadan da za su yi amfani da su wajen tayar da tarzoma, su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su, tare da amfani da kafafen sada zumunta wajen inganta zaman lafiya.

Shugaban Aminu Magashi Garba Foundation, Dakta Aminu Magashi Garba, ya jaddada aniyar gidauniyar na ci gaba da tallafa wa

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *