Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya buɗe rumfar baje kolinsa a taron makamashi na ƙasa da ƙasa na ADIPEC 2026 da ke gudana a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, domin gabatar da ayyukansa da damar zuba jari a fannonin hako mai, sarrafa shi da rarraba shi.
Taron, wanda aka fara ranar 2 ga Nuwamba kuma zai ƙare ranar 5 ga watan, ya samu halartar manyan jami’an Najeriya da suka haɗa da Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da mai, Sanata Heineken Lokpobiri; Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da iskar gas, Ekperikpe Ekpo; da wasu manyan jami’an ma’aikatar da hukumar kula da harkokin man fetur ta sama.
An buɗe taron ne da jawabin Ministan Masana’antu da Fasahar Zamani na UAE, kuma shugaban gudanarwa na kamfanin ADNOC, Dakta Sultan Ahmed Al Jaber, wanda ya bayyana muhimman batutuwan da za a tattauna a tsawon kwanaki huɗu na taron.
- ’Yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar Islamiyya 14 a Jihar Neja
- ’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da satar mota mai ɗauke da kayayyakin miliyoyin Naira a Maiduguri
Jim kaɗan bayan buɗe taron, NNPC ta buɗe rumfarta ga mahalarta daga ƙasashe daban-daban, inda ta gabatar da ayyukanta da damar zuba jari ga gwamnatoci, abokan hulɗa, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a harkar makamashi.
Daga cikin waɗanda suka fara ziyartar rumfar akwai shugaban kwamitin gudanarwar NNPC, Ahmadu Musa Kida, wasu mambobin kwamitin da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.
NNPC ta ce shugabanninta za su kuma gabatar da jawabai a tarukan dabaru da na fasaha, tare da tattaunawa da takwarorinsu na ƙasashen duniya da masu zuba jari kan makomar samar da makamashi.
Ana sa ran taron na ADIPEC 2026 zai haɗa mutane sama da 239,000 daga ƙasashe fiye da 170, ƙarƙashin jagorancin shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, kuma kamfanin ADNOC ne ya shirya shi.