Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta kashe wani da ake zargi da fashi da makami, tare da ƙwato motoci biyu da bindiga bayan musayar wuta da wasu ’yan fashi a jihar Ogun.
Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na dare a ranar 1 ga Nuwamba, 2026, a yankin Ijaba da ke Iyesi, Ota, lokacin da jami’an sintiri suka samu rahoton wani harin fashi da makami da ke gudana.
- ’Yan sanda sun gano gawar jami’ai biyar da ’yan bindiga suka kashe a Zamfara
- ’Yan sanda sun kuɓutar da mata masu shayarwa uku daga hannun masu garkuwa a Kogi
A cewar rundunar, da jami’an suka isa wurin, ’yan fashin sun buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, inda jami’an suka kashe ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin.
Ta ce sauran ’yan fashin sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da jami’an suka ƙwato bindiga ƙirar gida, harsasai biyu masu rai da kuma kwas ɗin harsasai bakwai da aka harba.
Haka kuma, rundunar ta ce ta ƙwato motoci biyu ƙirar Nissan Almera da Toyota Camry, tare da wasu kayayyakin da ake zargin an sace, ciki har da wayar Tecno, hotunan fasfo guda uku, katin layin MTN, Naira 4,000 da katunan NIN guda biyu. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.