Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta gano gawar jami’anta biyar da ’yan bindiga suka kashe a wani harin kwanton ɓauna a Jihar Zamfara, tare da kuɓutar da wasu jami’ai bakwai da suka tsira daga harin.

A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne a ranar 1 ga Nuwamba, 2026, lokacin da jami’an ke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Zamfara domin gudanar da aikin tsaro yayin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.

Rundunar ta bayyana cewa jami’an rundunar VCRU da sashen yaƙi da garkuwa da mutane ne suka gudanar da aikin bincike da ceto, inda suka gano gawar jami’ai biyar, tare da kuɓutar da wasu bakwai da ba su samu rauni ba.

Ta ƙara da cewa jami’ai biyu sun samu raunin harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sai dai rundunar ta ce maharan sun kwashe bindigogin AK-47 guda biyar na jami’an, yayin da jami’an tsaro na haɗin gwiwa ke ci gaba da bincike domin gano makaman da kuma cafke waɗanda suka kai harin.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *