Ɗan wasan ƙungiyar CD Tenerife ta ƙasar Sifaniya, Jesús de Miguel, ya rasu yana da shekara 30 bayan mummunan karo da ya yi da golan ƙungiyar FC Andorra yayin wasan da suka fafata a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026.

Lamarin ya faru ne a ƙarshen wasan gasar rukuni na biyu ta Sifaniya, lokacin da golan Andorra, Jesús Owono, ya fito daga cikin raga domin ƙoƙarin ƙwace ƙwallo, inda ya yi karo da De Miguel.

An ba golan jan kati kai tsaye bayan faruwar lamarin.

Ma’aikatan lafiya sun yi ƙoƙarin taimaka wa ɗan wasan a filin wasa na tsawon mintuna kafin a ɗauke shi zuwa asibiti cikin motar ɗaukar marasa lafiya.

An dakatar da wasan a mintunan ƙarshe, yayin da sakamakon wasan yake canjaraz 2-2.

Rahotanni sun ce De Miguel ya samu bugun zuciya bayan karon, kuma halin da yake ciki ya ƙara tsananta a asibiti kafin rasuwarsa da misalin ƙarfe 8 na safiyar Talata.

Rasuwar tasa ta jawo jimami a duniyar ƙwallon ƙafa, inda ƙungiyoyi da dama, ciki har da FC Andorra, Barcelona da Real Madrid, suka aike da saƙonnin ta’aziyya ga iyalansa da ƙungiyar Tenerife.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *