Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya kai ziyarar aiki hedikwatar rundunar soji ta 10 Division Garrison da ke Jalingo, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da jami’an tsaro.
A cewar kwamishiniyar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta jihar, Zainab Jalingo, ziyarar na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kefas na ci gaba da tattaunawa da hukumomin tsaro domin inganta zaman lafiya a faɗin jihar.
- ’Yan sanda sun gano gawar jami’ai biyar da ’yan bindiga suka kashe a Zamfara
- Tinubu ya fara biyan Super Falcons ladan Dala 100,000 bayan lashe WAFCON
Ta ce ziyarar za ta taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi da kuma tallafa wa ayyukan da ake gudanarwa domin tunkarar ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan da ke fuskantar barazanar rashin tsaro.
Gwamna Kefas ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen kare rayukan jama’a da al’ummomi, tare da samar da yanayin da zai ba da damar bunƙasar tattalin arziki.
Gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da ba da fifiko ga harkokin tsaro domin tabbatar da cewa al’ummar Taraba za su iya rayuwa, gudanar da ayyukansu da kuma neman hanyoyin samun ci gaba cikin zaman lafiya.