Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafa wa harkokin kasuwancin noma, musamman ga matasa masu zuba jari a fannin da sarrafa amfanin gona.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwar jihar karo na 566, inda ya karɓi Hajiya Saudatu Aliyu Mu’azu, wadda ta lashe kyautar ƙwarewa a fannin noma da sarrafa amfanin gona a gasar bayar da kyaututtukan ƙananan da matsakaitan sana’o’i ta ƙasa (National MSME Awards).
Bago ya taya Saudatu murna bisa nasarar, yana mai cewa ayyukanta na tallata jihar da Najeriya a cikin gida da wajen ƙasar.
- Gwamna Kefas ya gana da rundunar soji a Taraba kan ƙarfafa tsaro
- Tinubu ya fara biyan Super Falcons ladan Dala 100,000 bayan lashe WAFCON
Ya kuma ce gwamnatin jihar na yaba da gudummawar da take bayarwa, tare da ƙarfafa wasu su yi koyi da ita.
Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Usman, ya bayyana Saudatu a matsayin jakadiyar matasa a harkokin kasuwancin noma da sarrafa amfanin gona.
Ya ce ta shafe shekaru tana gudanar da noman amfanin gona, kiwon kaji, sarrafa kayayyakin gona da ƙera kayayyakin da ake iya sayarwa a kasuwa.
A nata jawabin, Saudatu ta ce shirinta na “Made in Niger” na da nufin tallata damar tattalin arzikin jihar, inda ta bayyana cewa ya ƙunshi ’yan kasuwa 6,433 da ke harkar sarrafa amfanin gona, tare da kayayyaki 100 da ake shirin tallatawa a kasuwannin ƙasashen waje.