Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce babbar hanyar Legas zuwa Calabar za ta taimaka wajen bunƙasa kasuwanci da samar da sabbin damarmakin tattalin arziki a jihohin da ta ratsa.
Uzodimma ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa bayan ƙaddamar da kamfen ɗin jam’iyyar APC na shugaban ƙasa a shiyyar Kudu maso Kudu, wanda aka gudanar a filin wasa na U.J. Esuene da ke Calabar, Jihar Cross River.
- ’Yan sanda sun kuɓutar da mata masu shayarwa uku daga hannun masu garkuwa a Kogi
- ’Yan sanda sun gano gawar jami’ai biyar da ’yan bindiga suka kashe a Zamfara
Ya ce aikin hanyar, wanda ya ratsa jihohi da dama, zai inganta haɗin kai tsakanin yankuna, da sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci.
Gwamnan ya kuma danganta aikin da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa manufofin gwamnatin na aza tubalin samun ci gaba mai ɗorewa.
Uzodimma ya jaddada cewa ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin ƙarƙashin shirin Renewed Hope na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.