Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya fara cika alƙawarin bai wa ’yan wasan tawagar Super Falcons ladan Dala 100,000, bayan da suka lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata ta 2025 (WAFCON).
Hukumar ƙwallon ƙafa Najeriya ce ta bayyana hakan, inda ta ce ’yan wasan sun fara karɓar kuɗin da ya kai kusan Naira miliyan 140, bisa alƙawarin da shugaban ƙasar ya yi musu bayan nasarar da suka samu a wasan ƙarshe da Morocco a watan Yulin 2025.
- ’Yan sanda sun gano gawar jami’ai biyar da ’yan bindiga suka kashe a Zamfara
- Ɗan Cristiano Ronaldo ya samu kiran farko zuwa tawagar Portugal ta ’yan ƙasa da shekara 17
Super Falcons ta lashe gasar ne a karo na 10 a tarihinta, bayan da ta doke Morocco a wasan ƙarshe na gasar da aka gudanar a ƙasar.
Kyaftin ɗin tawagar, Rasheedat Ajibade, ta gode wa Shugaba Tinubu bisa cika alƙawarin, tana mai cewa hakan ya nuna an yaba da nasarar da ƙungiyar ta samu da kuma gudummawarta ga ci gaban ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Biyan ladan na zuwa ne bayan kusan watanni huɗu da tawagar ta lashe gasar, yayin da ’yan wasan suka fara karɓar kuɗin da aka yi musu alƙawari.