Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta fara rabon kayan tallafin sana’o’i da abinci ga gidaje 653 da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Kebbi a shekarar 2025.
Daraktar Janar ta hukumar, Zubaida Umar, ce ta sanar da fara rabon tallafin a wani biki da aka gudanar a Birnin Kebbi ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, a ƙarƙashin shirin tallafin gwamnatin tarayya ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Zubaida, wadda Daraktan Sashen bayarda Agaji, Alhaji Abbani Imam Garki, ya wakilta, ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da shirin domin ƙara tallafa wa waɗanda suka yi asarar dukiyoyinsu, taimaka musu su farfaɗo da sana’o’insu da kuma ƙarfafa juriyar al’ummomi ga bala’o’i.
- Mataimakin gwamnan Sakkwato ya danganta goyon bayan APC da shugabancin Tinubu da Aliyu
- Tambuwal ya zargi gwamnatin Sakkwato da tauye ’yancin siyasar ’yan adawa
Ta bayyana cewa za a aiwatar da shirin a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da haɗin gwiwar hukumomin bayar da agajin gaggawa na jihohi da ƙananan hukumomi da sauran hukumomin gwamnati domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen rabon kayan tallafin.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da injinan ɗinki, injinan niƙa, babura masu kafa uku na ɗaukar kaya da nau’o’in kayan abinci.
Daraktar Janar ɗin ta buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayan yadda ya kamata domin farfaɗo da sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
A nasa jawabin, Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris, wanda Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Aliyu Umar, ya wakilta, ya gode wa Shugaba Tinubu da NEMA bisa tallafin.
Shi ma Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, wanda Ubandoman Gwandu, Alhaji Sadiq Ibrahim-Saad, ya wakilta, ya yaba da shirin tare da kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayan yadda ya dace.