Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Idris Mohammed Gobir, ya ce dimbin goyon bayan da jam’iyyar APC ke samu a jihar na nuna yadda al’umma ke jin daɗin shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu.
Gobir ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dubban mambobin ƙungiyoyin matasa da suka taru a gidan gwamnatin jihar, bayan gudanar da gangamin nuna goyon baya ga gwamnatocin APC.
- Gwamnatin Sakkwato ta ce ta ɗauki dubban matasa aiki, ta tallafa wa ’yan kasuwa
- ’Yan sanda sun sanar da sauya hanyoyin zirga-zirga a Lafia gabanin gangamin APC
- Majalisun dokoki 28 sun amince da kudirin kafa ’yan sandan jihohi
Ya ce gwamnatin jihar ta gudanar da ayyukan raya ƙasa da dama a sassa daban-daban na Sakkwato domin inganta rayuwar jama’a da bunƙasa tattalin arziki, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da aiwatar da ayyukan da al’umma za su amfana da su.
Mataimakin gwamnan ya kuma gode wa ’yan kasuwa, manoma, dattawa, matasa da mata bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar APC a jihar.
A nasu jawaban, Shugaban APC na jihar, Alhaji Haruna S. Gobir, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Gudummawar Lafiya ta Jihar Sokoto, Abu Abdulkarim, da Alhaji Nasir Italy, sun yaba wa gwamnatin Ahmed Aliyu kan ƙoƙarinta na bunƙasa matasa.