Majalisun dokokin jihohi 28 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da ke neman kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi, a cewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
A cikin wata sanarwa da magatakardar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ya fitar, ya ce adadin ya haura mafi ƙarancin jihohi 24 da ake buƙata domin amincewa da kudirin, bisa tanadin sashe na 9 na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
- Kamfanin siminti na Dangote ya tallafa wa ɗalibai 75 da tallafin karatu a Kogi
- NYSC ta musanta bayar da takardar shaida ga tsohon minista Geoffrey Nnaji
Sanarwar ta bayyana cewa an aika kudirin ga majalisun dokoki 36 na jihohin ƙasar ranar 16 ga Satumba, tare da ba su wa’adin kwanaki 30 domin nazari da amincewa da shi.
Ogunlana ya ce wa’adin ya ƙare ranar 15 ga Oktoba, kuma an kammala tantance rahotannin amincewar da majalisun jihohin suka bayar.
Ya ƙara da cewa ana gudanar da sauran matakai domin aika kudirin ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don ya sanya hannu a kansa.