Kamfanin siminti na Dangote, reshen Obajana da ke Jihar Kogi, ya bai wa ɗalibai 75 daga al’ummar Oworo tallafin karatu na miliyoyin Naira a shekarar 2026, a wani shiri na tallafa wa ilimi da ci gaban al’ummomin da ke maƙwabtaka da kamfanin.
Wannan ya kai ɗalibai 125 da kamfanin ya tallafa wa tsakanin shekarar 2025 da 2026, inda a shekarar da ta gabata ɗalibai 50 suka amfana, kafin adadin ya ƙaru zuwa 75 a bana.
Wakilin Daraktan Kamfanin, Mista Ademola Adeyemi, ya ce shirin na da nufin rage wa iyaye da masu kula da ɗalibai nauyin kuɗaɗen karatu.
Ya bayyana cewa ƙarin adadin waɗanda suka amfana na nuna ƙudurin kamfanin na bunƙasa ilimi da ƙarfafa matasa a yankunan da ke karɓar baƙuncinsa.
- ’Yan sanda sun kuɓutar da mata masu shayarwa uku daga hannun masu garkuwa a Kogi
- ADC ta ce babu gwamnan da ke da ikon hana jam’iyya gudanar da kamfen a jiha
Shirin ya kuma faɗaɗa tallafin da kamfanin ke bayarwa ga fiye da manyan al’ummomi biyar da ke kewaye da shi, wato Jakura, Oyo, Iwaa, Apata da Obajana.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Oworo, Mista Ibrahim Adoga, ya yaba wa kamfanin bisa gudummawar da yake bayarwa wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin ya haƙa rijiyoyin burtsatse guda biyar ga al’ummomi biyar a shekarar 2025, sannan ya ƙara wasu huɗu a shekarar 2026.
Da yake magana a madadin iyaye, Alƙali Ibrahim Eleson Denja ya nuna godiya ga kamfanin bisa ci gaba da shirin bayarda tallafin karatun.
Ita ma Oheda Faith Helen, ɗalibar nazarin Biochemistry a Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi da ke Lokoja, wadda ta yi jawabi a madadin waɗanda suka amfana, ta ce tallafin zai taimaka musu wajen cimma burinsu na karatu tare da rage nauyin kuɗaɗe ga iyalansu.
Taron ya samu halartar jami’an gwamnati, shugabannin al’umma da wakilan kwamitin kula da tallafin ilimi na Oworo, ciki har da Injiniya E. O. Olaitan Femi da wakilin Olu na Oworo.