Jam’iyyar ADC ta ce babu wani gwamna da ke da ikon hana jam’iyya gudanar da kamfen ko hana ’yan takara bayyana ra’ayoyinsu, yayin da take zargin gwamnatin Jihar Sokoto da katsalandan a harkokin siyasarta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar 3 ga Nuwamba, 2026, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya ce ADC na gargadin gwamnatin jihar kan duk wani yunƙuri na kawo cikas ga shirin ƙaddamar da kamfen ɗinta a Sokoto.
Jam’iyyar ta ce gudanar da kamfen da wayar da kan masu zaɓe haƙƙi ne da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba jam’iyyun siyasa, don haka babu wani mai riƙe da mukamin gwamnati da ya isa ya hana su gudanar da harkokinsu na siyasa.
- ’Yar kasuwar Neja ta lashe kyautar ƙwarewa kan bunƙasa noma da sarrafa amfanin gona ta ƙasa
- Majalisar Kano ta tabbatar da nadin Gani da Bature a matsayin kwamishinoni
ADC ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta daina abin da ta kira ƙoƙarin tsoratar da ’yan adawa, tare da buƙatar hukumomin tsaro da sauran cibiyoyin gwamnati su yi aiki bisa kundin tsarin mulki da muradun al’ummar Najeriya, ba tare da nuna bambanci ga jam’iyya ba.
Ta gargaɗi cewa za ta ɗora wa Gwamnan Sokoto alhakin duk wani tashin hankali ko hari da aka kai wa ’yan adawa, tare da cewa ba za ta fasa gudanar da kamfen ɗinta a jihar ba.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci mambobinta da magoya bayanta su kasance masu bin doka da oda a duk lokacin gudanar da harkokin siyasa.