Hukumar yi wa matasa hidimar ƙasa (NYSC) ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa ba ita ce ta bayar da takardar shaidar NYSC da ake dangantawa da tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Geoffrey Nnaji, ba.

Mataimakin daraktan sashen bayar da takardun shaida na hukumar, Yusuf Abubakar Jumare, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayar da shaida a matsayin mashedu na biyu na masu gabatar da ƙara a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik.

Ya ce binciken da sashen ya gudanar ya tabbatar da cewa takardar ba ta gaskiya ba ce.

Hukumar ICPC ce ta gurfanar da Nnaji bisa zargin ƙirƙirar takardar shaidar karatu da halasta kuɗaɗen haram.

Tsohon ministan shi ne ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan Jihar Enugu mai zuwa.

Jumare ya ce sashen ya fara binciken ne bayan samun buƙata daga hukumar ICPC, inda bayyana cewa takardar, wadda ake zargin an bayar a shekarar 1985, tana ɗauke da wasu bayanai da ba su dace da tsarin hukumar a lokacin ba, ciki har da lambar shaida mai harafin “A”, alhali NYSC ba ta fara amfani da wannan tsarin ba sai a shekarar 1990.

Ya kuma bayyana cewa lambar kiran hidimar da ke jikin takardar tana da lambobi huɗu, alhali ta shekarar 1985 tana da lambobi biyar.

Haka kuma, takardar ta nuna watanni 13 na hidima maimakon watanni 12, sannan ba ta ɗauke da sa hannun Darakta-Janar na NYSC da ke kan muƙami a lokacin.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da takardun wasiƙu tsakanin ICPC da NYSC kan takardar shaidar, waɗanda kotun ta amince da su a matsayin hujjoji.

Lauyoyin Nnaji sun ce za su gabatar da ƙorafinsu kan karɓar waɗannan takardu a wani lokaci, inda Mai Shari’a Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 30 ga Nuwamba domin ci gaba da yi wa mashedu tambayoyi, sannan zuwa 29 ga Janairu domin ci gaba da sauraron shari’ar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *