Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta sanar da rufe wasu tituna tare da sauya hanyoyin zirga-zirga a wasu sassan birnin Lafia, gabanin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026, yayin ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Rahman Namsel, ya fitar, ya ce ana sa ran gangamin zai samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar da kuma magoya bayan APC.

Sanarwar ta ce rundunar ta tanadi matakan tsaro da kula da zirga-zirga domin kare shugaban ƙasa da tawagarsa, mahalarta gangamin da sauran al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda kafin taron, lokacin gudanar da shi da kuma bayansa.

Rundunar ta ƙara da cewa za a sauya hanyoyin zirga-zirga tare da takaita motsin ababen hawa a wasu hanyoyi da wurare da aka ware a cikin birnin Lafia.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shetima Jauro Mohamed, ya buƙaci mazauna Lafia da su kwantar da hankalinsu, su yi haƙuri tare da ba da haɗin kai a lokacin da za a gudanar da waɗannan matakai.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *