Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci sabon Sakataren Janar na Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Samson Adamu, da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa a nahiyar.

Shettima ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi Adamu, wanda ya zama ɗan Najeriya na farko da ya riƙe muƙamin Sakataren Janar na CAF, inda ya ce naɗin nasa ya ƙara tabbatar da irin baiwa da ƙwarewar da ’yan Najeriya ke da su a fagen wasanni na duniya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci sabon sakataren ya yi aiki da nagartaccen shugabanci da kishin hidima, yana mai cewa nasarorin Najeriya a wasanni sun samo asali ne daga ƙwarewar ’yan ƙasa, jajircewar masu gudanar da wasanni da kuma cibiyoyin da ke gano tare da bunƙasa baiwar matasa.

A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Shehu Dikko, ya bayyana naɗin Adamu a matsayin wani muhimmin ci gaba a harkokin gudanar da wasanni a Najeriya.

Dikko ya kuma nuna godiya ga gwamnatin tarayya bisa amincewa da Najeriya ta karɓi baƙuncin babban taron CAF da bikin bayar da kyaututtukan hukumar, waɗanda za a gudanar a watan Nuwamba da Disamban 2026, bi da bi.

An naɗa Samson Adamu a matsayin Sakataren Janar na CAF ne a ranar 1 ga Nuwamba, 2026, bayan kammala aikin ɗaukar ma’aikata da hukumar ta gudanar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *