Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta dakatar da alƙalai uku na tsawon shekara guda ba tare da albashi ba, bayan wani taronta karo na 112 da ta gudanar a Abuja.

Alƙalan da abin ya shafa sun haɗa da Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir ta Babbar Kotun Jihar Nasarawa, Babban Alƙali Mohammed Sani Salihu na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa da Mai Shari’a Sobere Biambo na Babbar Kotun Jihar Ribas.

Majalisar ta kuma hana Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir samun ƙarin matsayi na tsawon shekaru uku, sannan ta sanya irin wannan takunkumi ga Mai Shari’a Sobere Biambo kan bayar da umarnin kama mutane da kuma cin tarar masu shigar da ƙara a rikicin farar hula ba tare da bin ƙa’ida ba.

NJC ta kuma aika wasiƙun gargaɗi ga wasu jami’an shari’a uku, tare da yi wa wasu takwas gargaɗi kan halayensu ko ayyukansu.

Haka kuma, ta umarci Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta Jihar Imo da ta saka Mukaddashiyar Babbar Alƙaliyar jihar, Mai Shari’a Ijeoma Agugua, cikin jerin waɗanda za a yi wa hira domin naɗa Babbar Alƙaliyar jihar ta din-din-din.

Bugu da ƙari, majalisar ta ba da shawarar naɗa mutane 28 a muƙaman shari’a.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *