Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta taya tsohon ɗan wasanta, Cristiano Ronaldo, murnar kammala wakiltar ƙasar Portugal a matakin ƙasa da ƙasa, bayan shafe shekaru 23 yana bugawa tawagar ƙasar wasa.
A cikin saƙon da ta wallafa, ƙungiyar ta taya shi murna bisa irin nasarorin da ya samu, inda ta bayyana cewa ya buga wasanni 234 tare da zura ƙwallaye 146 wa Portugal.
Ronaldo ya fara wakiltar Portugal a shekarar 2003, kuma ya taimaka wa ƙasar lashe gasar Euro 2016 da kuma UEFA Nations League a shekarar 2019 da 2025.
- Cristiano Ronaldo ya sanar da yin ritaya daga buga wa Portugal wasa
- NJC ta dakatar da alƙalai uku tsawon shekara guda ba tare da albashi ba
Ya kuma kafa tarihi a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wa ƙasar wasa da zura ƙwallaye a matakin ƙasashen duniya na maza.
Ronaldo ya taɓa taka leda a Manchester United a lokuta biyu, daga 2003 zuwa 2009 da kuma 2021 zuwa 2022. A zamansa na farko, ya lashe kofuna da dama, ciki har da gasar Premier League sau uku da Champions League sau ɗaya.
A halin yanzu, Ronaldo mai shekara 41 yana taka leda a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, yayin da bankwana da tawagar Portugal ke kawo ƙarshen wata muhimmiyar tafiya a tarihin ƙwallon ƙafarsa.