Tawagar matan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 17, Flamingos, ta samu tikitin zuwa wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta mata, bayan da ta doke Brazil da ci 3-1 a wasan kusa da na karshe da suka buga ranar Laraba.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya ta kai wasan karshe na gasar, bayan da ta shafe shekaru tana fafutukar cimma wannan buri.
‘Yan wasan Flamingos sun nuna bajinta a wasan da aka gudanar a filin wasa na Mohammed VI Football Complex da ke birnin Rabat na Marokko.
-
Shettima ya buƙaci sabon Sakataren CAF, Samson Adamu, ya yi bajinta a muƙaminsa
-
Tinubu ya fara biyan Super Falcons ladan Dala 100,000 bayan lashe WAFCON
-
Ɗan Cristiano Ronaldo ya samu kiran farko zuwa tawagar Portugal ta ’yan ƙasa da shekara 17
A farkon wasan, Najeriya ta fara kai hare-hare ta hannun Oluwakemi Adegbuyi da Oluebube Umejiaku, yayin da Queen Joseph ta kusa zura kwallo a ragar Brazil a minti na 21, amma mai tsaron ragar Brazil ta tare harin.
An tafi hutun rabin lokaci ne ba tare da kowace tawaga ta zura kwallo ba, duk da damar da bangarorin biyu suka samu.
Sai dai Najeriya ta dawo da sabon kuzari a zagaye na biyu, inda Queen Joseph ta fara jefa kwallo a ragar Brazil a minti na 56, lamarin da ya sanya magoya bayan Najeriya farin ciki.
Daga nan ne Awawu Bashiru ta kara wa Najeriya kwallaye biyu, inda ta zura ta farko a minti na 71, kafin ta sake jefa ta uku a minti na 80.
Wannan bajinta ta tabbatar da rinjayen da Najeriya ta yi a wasan, inda ta samu damar kai hare-hare har sau 30.
Brazil ta samu kwallon ta ne a minti na 89 ta hannun Greise Kelly, amma hakan bai hana Flamingos samun nasarar da ci 3-1 ba.
Nasarar ta kafa tarihi ga tawagar Najeriya, wadda a baya ta taba kai wa matakin kusa da na karshe, inda ta kare a matsayi na uku a gasar da aka gudanar a Indiya shekaru hudu da suka wuce.
Yanzu haka Flamingos za ta kara da Japan a wasan karshe, bayan da Japan ta fitar da zakarun gasar na bara, Koriya ta Arewa, a bugun fenareti.
Wasan karshe zai bai wa Najeriya damar lashe kofin duniya na ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 17 a karon farko.