Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, da Sarkin Benin, Oba Ewuare II, sun bayyana goyon bayansu ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) wajen yaƙi da matsalar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi.
Sun bayyana hakan ne yayin ziyarar wayar da kan jama’a da shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa, ya kai birnin Benin.
Gwamna Okpebholo ya yi alƙawarin haɗa kai da hukumar, yana mai cewa miyagun ƙwayoyi na taimakawa wajen ƙara aikata laifuka.
- Shettima ya nemi al’ummar Nasarawa su sake zaɓen Tinubu da sauran ’yan takarar APC
- ’Yan sanda sun yi barazanar kama masu lalata fastocin ’yan takara a zaɓen 2027
Saboda goyon bayan da ya nuna, hukumar ta naɗa gwamnan a matsayin babban jakadan shirin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na WADA.
A yayin ziyarar fadar Sarkin Benin, Marwa ya nemi haɗin gwiwar sarakunan gargajiya, malaman addinai da sauran masu ruwa da tsaki wajen yaƙi da matsalar.
Ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan 15 na fama da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Shugaban hukumar ya kuma ce suna faɗaɗa wani shiri da ke ƙarfafa manoman wiwi su koma noman amfanin gona na halal kamar rogo, doya da masara, tare da tallafin gwamnati.