Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya ce ana shirin miƙa kudirin dokar kafa ’yan sandan jihohi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sanya hannu, wanda zai ba da damar kafa rundunonin ’yan sanda a matakin jihohi.

A wani zaman majalisar, ’yan majalisar sun kuma amince da kudirin gyara dokar kula da lafiya ta ƙasa (National Health Act) a karatu na biyu, domin ƙarfafa ayyukan agajin gaggawa a fannin lafiya.

Haka kuma, kudirin dokar hana karɓar kuɗin hayar gida na shekaru da dama a lokaci guda a Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya tsallake karatu na biyu a majalisar.

Wannan na nufin kudurorin biyu da suka shafi lafiya da haya za su ci gaba da bin matakan majalisa kafin a yanke hukuncin amincewa da su a matsayin doka.

Sai dai majalisar ba ta bayyana ƙarin bayani kan lokacin da za a miƙa kudirin dokar kafa ’yan sandan jihohi ga shugaban ƙasa ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *