Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci al’ummar jihar Nasarawa da su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Shettima ya yi wannan kira ne a wajen taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar a jihar Nasarawa, inda ya nemi jama’a su ci gaba da goyon bayan jam’iyyar.
- Sojoji sun kashe waɗanda ake zargi da garkuwa da mutane uku a Kogi
- Shettima ya buƙaci sabon Sakataren CAF, Samson Adamu, ya yi bajinta a muƙaminsa
Ya bayyana gyaran hanyoyi da sauran ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ta gudanar a matsayin wasu daga cikin dalilan da ya kamata jama’a su sake ba gwamnatin damar ci gaba da mulki.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce goyon bayan Tinubu da sauran ’yan takarar APC zai ba su damar ci gaba da aiwatar da ayyukan raya ƙasa da suka fara.
Wannan kira na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen da ke tafe.