Gidan rediyon Blueprint Radio ya bayyana alhininsa kan rasuwar ’yar jarida Zainab Rabiu Salisu, wadda ta rasu a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026.
Rasuwar Zainab ta jefa ’yan uwanta, abokan aikinta da sauran masu ruwa da tsaki a kafafen yaɗa labarai cikin jimami, musamman waɗanda suka yi aiki tare da ita a gidan rediyon Express FM da ke Kano.
Tsohon Editan Labarai na Express FM, Adamu Aminu, ya bayyana cewa Zainab ta kasance ƙwararriyar ma’aikaciya mai ƙwazo, son koyon aiki da kuma fara’a tun lokacin da aka kafa gidan rediyon a shekarar 2014.
- NJC ta dakatar da alƙalai uku tsawon shekara guda ba tare da albashi ba
- Kwastam ta ƙaddamar da tsarin tantance kaya ta intanet domin rage jinkirin fitar da kaya a tashar Apapa
Ya ce ta kasance mai sauƙin kai da barkwanci, tana kuma mutunta abokan aikinta, inda ya bayyana cewa ko bayan sauya mata sashe daga ɗakin labarai zuwa sashen siyasa, ta ci gaba da ziyartar tsoffin abokan aikinta.
Adamu ya kuma bayyana cewa hirar da suka yi kusan makonni biyu kafin rasuwarta ita ce ta ƙarshe a tsakaninsu, inda ta kira shi ta wayar wani tsohon abokin aiki domin gaishe shi da bayyana kewarsa tun bayan komawarsa Abuja.
Blueprint Radio na miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar, abokan aikinta da dukkan ma’aikatan Express FM, tare da addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya sanya Aljannatul Firdaus ce makomarta. Amin.