Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan shugabancin jam’iyyar ADC domin kawo cikas ga burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da kuma raunana tasirin ’yan adawa.
Atiku ya bayyana cewa hukuncin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan dubban magoya bayansa sun tarbe shi a Sakkwato yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC.
Ya yi zargin cewa matakin wani yunkuri ne na rage masa goyon baya a Arewa da kuma hana yaƙin neman zaɓensa yaɗuwa zuwa sauran sassan ƙasar.
- Kwastam ta ƙaddamar da tsarin tantance kaya ta intanet domin rage jinkirin fitar da kaya a tashar Apapa
- NJC ta dakatar da alƙalai uku tsawon shekara guda ba tare da albashi ba
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Alhamis, Atiku ya ce tarbar da aka yi masa a Sakkwato na nuna yadda ’yan Najeriya ke neman sauyin gwamnati saboda tsadar rayuwa.
Ya kuma jaddada cewa takararsa ba ta Arewa kaɗai ba ce, domin matsin tattalin arziki ya shafi al’umma a dukkan yankunan ƙasar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma nuna shakku kan sake buɗe batun rikicin shugabancin ADC, duk da wani hukuncin da Mai Shari’a Musa Liman na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a baya, a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025.
Ya ce kotun ta yi watsi da ƙalubalen da aka shigar kan shugabancin David Mark bisa batutuwan hurumin kotu, cancantar masu ƙarar da kuma rashin kammala hanyoyin warware rikici na cikin gida, tare da warware wasu batutuwan ƙarar a madadin waɗanda ake ƙara.
Atiku ya ce jam’iyyarsa za ta ƙalubalanci sabon hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, tare da kira ga magoya bayanta su kasance masu bin doka da oda.
Ya kuma tabbatar da cewa shirin yaƙin neman zaɓen ADC mai taken “Affordable Life” wato samar rayuwa mai kyau zai ci gaba, inda ya bukaci magoya bayansa su kai saƙon jam’iyyar gida-gida, musamman yayin da tawagar yaƙin neman zaɓen ke shirin zuwa Jihar Kebbi.