Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya buƙaci kwamishinonin yaɗa labarai na APC a jihohi su ƙarfafa haɗin gwiwa wajen isar da bayanan gwamnati da kuma wayar da kan al’umma kan manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Idris ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a wani taro da ya gudanar da kwamishinonin a Abuja, inda ya bayyana ingantaccen sadarwa a matsayin muhimmin ginshiƙi na shugabanci da gudanar da mulki.
Ya ce ya kamata a tabbatar ’yan Najeriya sun fahimci manufofi, ƙalubale da kuma amfanin shirin Renewed Hope Agenda, wanda ya ce gyare-gyaren da ke cikinsa na da nufin ƙarfafa tattalin arziki, faɗaɗa damarmaki, inganta ababen more rayuwa da bunƙasa ƙasa.
- Atiku ya zargi APC da amfani da hukuncin kotu wajen dakile takararsa ta 2027
- NJC ta dakatar da alƙalai uku tsawon shekara guda ba tare da albashi ba
Ministan ya kuma buƙaci kwamishinonin su ƙarfafa sadarwa tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi, su riƙa musayar sahihan bayanai tare da amfani da kafafen yaɗa labarai na gargajiya da na zamani.
Ya gargaɗe su kan yaɗa bayanan ƙarya da na yaudara, yana mai cewa gaskiya da bayyana bayanai a sarari na da muhimmanci wajen kiyaye amincewar jama’a.
Haka kuma, Idris ya jaddada cewa sadarwa ba ta tsaya ga isar da saƙon gwamnati kawai ba, domin ya kamata a riƙa sauraron koke-koken jama’a da fahimtar ra’ayoyinsu, tare da amfani da bayanan da aka samu wajen tsara yadda gwamnati za ta riƙa hulɗa da su.
Taron ya samu halartar kwamishinonin yaɗa labarai 20 daga jihohin da APC ke mulki, inda suka tattauna hanyoyin inganta haɗin gwiwa tsakanin matakan gwamnati, daidaita bayanan da ake yaɗawa da kuma ƙarfafa hulɗa da al’umma.