A cikin saƙon taya murnar da ya sanya wa hannu da kansa, Tinubu ya bayyana Iji a matsayin fitaccen ɗan Najeriya wanda ya shafe shekaru yana yi wa ƙasa hidima, tare da nuna kishin ƙasa da jajircewa.
Shugaban ƙasar ya ce ya san jakadan tsawon shekaru da dama, inda suka yi aiki tare a jam’iyyun siyasa daban-daban, ciki har da SDP a farkon shekarun 1990, Alliance for Democracy, Action Congress da APC.
- Kotu ta yi watsi da ƙarar Maihaja, ta tabbatar da nasarar Baba Mallam Wali
- Hukumar Kwastam ta tara Naira tiriliyan 1.42 cikin watanni biyu
Tinubu ya kuma yaba wa Iji bisa gudunmawar da ya bayar wajen kafawa da bunƙasa waɗannan jam’iyyu, tare da bayyana irin ayyukan da ya gudanar a matsayin malami, lauya da jagoran ƙungiyar ƙwadago.
Ya ce Iji na wakiltar Najeriya cikin mutunci a ƙasashen waje, inda a halin yanzu yake jakadan ƙasar a Rasha, tare da wakilci a Belarus, Kazakhstan, Uzbekistan, Kyrgyzstan da Turkmenistan.
Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ƙwarewa da gogewar jakadan wajen ƙarfafa dangantakar Najeriya da sauran ƙasashe, tare da yi masa fatan ƙarin shekaru cikin ƙoshin lafiya, farin ciki da nasara.