Ƙungiyar Kano First Youth Agenda da al’ummar Rimin Kebbe sun kai ziyarar godiya ga rundunar ’yan sandan Jihar Kano bisa ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da ’yan daba da sauran laifuffuka a jihar.

Ƙungiyar matasan, ƙarƙashin jagorancin Abbas Tijjani Bala Kalarawi, mai ba Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan harkokin ƙarfafa matasa, ta yaba wa Kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da tsaro.

Haka kuma, al’ummar Rimin Kebbe sun yaba wa jami’an ’yan sanda, musamman na sashen Zango, bisa cafke waɗanda suka bayyana a matsayin jagororin ayyukan daba a yankin.

Sun ce yanzu suna samun kwanciyar hankali.

Da yake mayar da martani, kwamishinan ’yan sandan ya bukaci matasa su zama jakadun gari na gari, yayin da ya jaddada cewa tabbatar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Ya kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa rundunar bayanan sirri masu inganci domin taimakawa yaƙi da laifuffuka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *