Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin samar da takin zamani mai rahusa da kuma injinan ban ruwa masu amfani da iskar gas na CNG ga manoman jihar Jigawa, a wani mataki na rage kuɗaɗen noma da kuma bunƙasa samar da abinci.

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ne ya bayyana hakan yayin isar da saƙon Shugaba Bola Tinubu a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar APC na shekarar 2027, a garin Hadejia.

Namadi ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kuma kafa cibiyoyin samar da iskar gas na CNG a sassan jihar domin sauƙaƙa wa manoma samun makamashin da ba fetur ba, tare da rage kuɗaɗen ban ruwa.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu na shirin sayo takin zamani da yawa domin sayar wa manoma a farashi mai rahusa, tare da samar musu da injinan ban ruwa masu amfani da iskar gas na CNG.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na da shirin sayen amfanin gona daga manoma ta hannun Hukumar Kasuwancin Kayayyakin Noma ta Najeriya (Nigerian Commodity Exchange), a farashin da aka amince da shi tun da farko, domin kare manoma daga asara da kuma ƙara musu kuɗaɗen shiga.

Ya ce an tsara waɗannan matakai ne domin sa harkokin noma su zama masu riba, ƙara yawan abincin da ake nomawa da kuma inganta rayuwar al’ummomin da suka dogara da noma.

A yayin gangamin, Gwamnan ya bayyana nasarorin gwamnatinsa a fannonin samar da ayyukan yi, ilimi, bunƙasa tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma da makamashi.

Ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan raya ƙasa idan aka sake zaɓensa, tare da kira ga mazauna mazabar Sanatan Arewa maso Gabashin jihar da su marawa Shugaba Tinubu da sauran ‘yan takarar APC baya a babban zaɓen shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *