Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron siyasa a Mapo Hall, Ibadan, Jihar Oyo, inda ya ce ya gudanar da taron cikin yanayin jimami saboda iyalan waɗanda suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa.
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada ƙudirin inganta kiwon lafiya
- Wike ya sanar da shirin ɗaukaka wasu masarautu a Abuja a watanni masu zuwa
Ya ce kamfanin Yutong, wanda ya bayyana a matsayin babban kamfanin kera motocin bas a duniya, ya sanya hannu kan yarjejeniyar kafa masana’antar haɗa motocin bas masu amfani da iskar CNG a tsohuwar masana’antar Leyland da ke Ibadan, domin samar da ayyukan yi da rage kuɗin sufuri.
Tinubu ya kuma ce ana sake gina hanyar Ijebu-Ode da siminti, tare da amincewa da kuɗin kammala hanyar Oyo zuwa Ogbomoso.
Ya kuma gabatar da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaɓen 2027.