Gwamnatin Jihar Kaduna ta jaddada ƙudirin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar, tare da yin kira ga ƙungiyoyin ƙwararru da su haɗa kai da ita wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana hakan yayin bikin cika shekaru 50 da kafa Ƙungiyar Likitocin Mata ta Najeriya (MWAN), reshen Kaduna.

Ta ce gwamnatin Gwamna Uba Sani na zuba jari wajen kayayyakin kiwon lafiya, magunguna da ma’aikatan lafiya, tana mai cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya biyan dukkan buƙatun al’umma ba.

Ta yabawa ƙungiyar bisa gudummawar da ta bayar tsawon shekaru 50, yayin da Darakta-Janar na KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya ce an yi wa dukkan ɗaliban makarantar masu buƙatu na musamman rajista a tsarin inshorar lafiya na jihar.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *