Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce za a ɗaukaka wasu masarautu a Abuja a watanni masu zuwa, bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗaukaka sarakunan gargajiya 16 zuwa matsayin aji na ɗaya da na biyu.

Wike ya bayyana cewa ya miƙa wa sarakunan takardun shaidar girma, wasiƙun naɗi, sandunan sarauta da sabbin motocin SUV a madadin shugaban ƙasa.

Ya ce sarakunan sun fito ne daga masarautu 16 da ke cikin Abuja.

Ya tuna cewa tun bayan kafa Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Abuja a shekarar 1997, masarautar Ona na Abaji ce kaɗai aka taɓa ɗaukaka matsayinta, lamarin da ya sa sauran sarakuna suka shafe shekaru suna jiran irin wannan dama duk da hidimar da suke yi wa al’ummominsu.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ne ya amince da ɗaukaka sarakunan a ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, yana mai jaddada cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da samar da yanayin gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya kuma ce za a tanadi kuɗin gina fadojin sarakunan aji na ɗaya a kasafin kuɗin 2027, kafin daga bisani a faɗaɗa shirin zuwa sarakunan aji na biyu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *