Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara za su samar da ayyukan yi, rage kuɗin sufuri da kuma sauƙaƙa tsadar abinci ga al’ummar Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron siyasa a Mapo Hall, Ibadan, Jihar Oyo, inda ya ce ya gudanar da taron cikin yanayin jimami saboda iyalan waɗanda suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa.

Ya ce kamfanin Yutong, wanda ya bayyana a matsayin babban kamfanin kera motocin bas a duniya, ya sanya hannu kan yarjejeniyar kafa masana’antar haɗa motocin bas masu amfani da iskar CNG a tsohuwar masana’antar Leyland da ke Ibadan, domin samar da ayyukan yi da rage kuɗin sufuri.

Tinubu ya kuma ce ana sake gina hanyar Ijebu-Ode da siminti, tare da amincewa da kuɗin kammala hanyar Oyo zuwa Ogbomoso.

Ya kuma gabatar da Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *