Kungiyar kare haqqin Dan Adam ta (Human Rights Watch) ta zargi sojojin Rwanda da kungiyar M23 da aikata manyan laifukan take hakkin Dan adam a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

A cewar kungiyar laifukan sun hada da tilasta yara shiga aikin soji, tsare mutane ba bisa ka’ida ba, azabtarwa, da kashe fararen hula da sojojin da aka kama daga tsakiyar shekarar 2024 zuwa Disambar 2025.

A cikin wani rahoto mai shafi 78 da kungiyar ta fitar, ta ce an kama dubban mutane, ciki har da yara masu shekaru 12, a yankunan kudu da arewacin Kivu.

An kai su sansanonin tsarewa da horo a yankunan Rumangabo da Tshanzu, inda ake azabtar da su ta hanyar duka, tilastawa, yunwa, da kuma  kashewa kai tsaye a wasu lokutan.

Wasu tsofaffin mutane da aka tsare sun  zargi sojojin Rwanda da hannu a wadannan ayyukan.

Human Rights Watch ta ce  yawan Rundunar Sojojin Rwanda a yankin, na  nuna cewa suna da cikakken iko a wurin, kuma hakan na iya sa su dauki alhakin aikata laifukan yaki.

Rahoton ya kara da cewa daruruwan mutane na iya rasa rayukansu a sansanonin, sannan ya yi kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa, da daukar matakan doka kan wadanda suka aikata laifukan.

Kungiyar ta kuma bukaci kasashen duniya su matsawa kasar Rwanda da mayakan M23 lambar dakatar da cin zarafin Dan adam da suke yi, da bayar da damar daukar matakan shari’a akan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *