Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dakile safarar mata masu juna biyu da ke neman haihuwa a kasar.
Ma’aikatar tace ta dauki wannan mataki ne domin cigaba da kare kima da mutuncin zama dan kasar, ta hanyar kawo karshen dabarun haihuwa ba bisa ka’ida ba da baki ke yi.
Gwamnatin Shugaba Trump tace ba zata a amince wani bako ya sami bizar ziyara da nufin zuwa ya haihu a Amurka, domin jaririnsa ya samu takardun zama dan kasa ba.
-
Tinubu ya taya Firaiminista Nerandramodi murnar zango Uku a mulki
-
Mbappé na da damar karya manyan tarihi 4 a gasar Kofin Duniya ta 2026
Wani ofishin jakadancin Amurka da ke Yammacin Afirka ya bankado wata badakalar hanyar safarar mata masu juna biyu da ta kunshi baki mazauna kasashen waje sama da 100.
Binciken ya gano yadda mutanen suka yi amfani da jabun takardu wajen neman biza, da nufin ganin ’ya’yansu sun zama ’yan kasar Amurka.
“Mun rushe wannan dandalin, mun soke bizar baki ’yan kasashen wajen, kuma muna hadin gwiwa da hukumomi domin gano wasu, tare da dakile yunkurin su baki daya” -inji Ofishin Jakadancin
A can nahiyar Turai ma, Ofishin Jakadancin Amurka ya gano sama da mutane 400 da ake zargi da wannan dabi’a ta neman haihuwa a Amurka tun daga shekarar 2024.
Masu bincike sun gano cewa al’amarin yana da alaka da aƙalla kamfanoni guda shida, da ke koya wa masu neman bizar abin da za su fada lokacin zuwa neman Bizar.
Sannan Binciken ya gano yadda kamfanonin ke tsara musu masauki, da kuma yadda zasu haihu a Amurka.
Haka zalika, wani ofishin jakadancin Amurka da ke Arewacin Afirka ya soke biza sama da 100, na iyayen da suka shiga kasar da burin haihuwa domin ‘ya’yansu su zama ‘yan kasa.
Jami’an kula da biza ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin tsaro da kuma amfani da fasahar tantance bayanai, sun gano hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen tafka wannan magudi, tare da yiwa tufkar hanci.
Samun bizar Amurka wata dama ce ta musamman, da bata zama dole ba, wannan ta sanya Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka daukar matakai masu tsauri a fadin duniya domin kawo karshen lamarin.
Amurka na kallon hakan a matsayin zagon kasa, shi yasa take tarwatsa cibiyoyin safarar mata masu juna biyu, da kuma hukunta duk wanda ya yi yunkurin tafka magudi a tsarin ta.
