An kafa Gidan Rediyo Najeriya kaduna na ne domin kare martabar Al'ummar Arewa

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Zaria Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana cewa Rediyo Najeria Kaduna ta kasance murya mai tasiri wadda ta taimaka wajen gina asalin al’adu, zamantakewa da siyasar Arewacin Najeriya.

Farfesa Ahmed ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da littafi mai taken “Rediyo Nigeria Na Kaduna: Abin Alfaharin Yan Arewa”, wanda wani ma’aikacin jami’ar, Malam Garba Abubakar Abdulkarim Kumo, ya rubuta.

Farfesa Adamu wanda ya samu wakilcin Mai taimaka masa a harkokin gudanarwa, Farfesa Bello Sabo ya ce littafin zai taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi, al’adu da kuma gidan Radio Nigeria Kaduna domin amfanin al’ummomi masu zuwa.

Ya ƙara da cewa, a mahangar Jami’ar ABU, Radio Nigeria Kaduna ba tashar rediyo ce kawai ba, illa wata rayayyar cibiya  mai tarihi da tasiri.

A cewarsa, irin wannan gado mai ɗorewa abu ne da jami’ar ke alfahari da shi kuma ya kamata a yi murna da shi baki ɗaya.

Shugaban Jami’ar ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa littafin zai zama muhimmin tushen samar da bayanai ga manazarta da masana, masu binciken tarihi, ‘yan jarida da duk masu kishin al’adun Arewacin Najeriya.

Marubucin littafin, Malam Garba Abubakar Abdulkarim Kumo, ya ce tunanin rubuta littafin ya fara ne kusan shekaru 20 da suka gabata lokacin da yake aiki a Radio Nigeria Kaduna

Kumo, wanda yanzu yake riƙe da mukamin Mataimakin Magatakarda a Jami’ar Ahmadu Bello, ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kan rubutun littafin kafin a buga shi.

A nasa sakon, Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, wanda Wazirin Zazzau, Alƙali Mohammed Inuwa Aminu ya wakilta ya taya marubucin murna bisa ƙoƙarinsa na adana ɗaya daga cikin manyan abubuwan tarihi da marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya bari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *