Hukumar Kula da Almajirai da Yaran da ba su zuwa Makaranta (NCAOOSCE) ta ce kimanin Almajirai da masu karamin karfi dubu 90 ne suka rabauta da naman Salla a bana.
Cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ta Nura Muhammad ya aikewa manema labarai, yace Makarantun Tsangaya 750 ne suka amfana a Babban Birnin Tarayya Abuja da jihohin Nasarawa, Neja, Kaduna, Bauchi, Filato da Yobe.
- Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin yaki da cutar Ebola
- ‘Yan Sanda sun kwato makamai a Kano
- RANAR DEMOKRADIYYA 2026: Ginin Ƙasa Da Haɗin Kai – Mohammed Idris
Sanarwar tace ta samu hadin kai daga Malaman Tsangayu, lamarin da ya kai ga samun nasarar aikin cikin tsari.
Ta jaddada aniyar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta walwala, haɗin kai da ci gaban Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan.
An gudanar da wannan shiri ne tare da tallafin kungiyar bada tallafi ta (Fountain Humanitarian Foundation) da (Türkiye Diyanet Foundation) a cewar hukumar.