Ministan ya jinjinawa manyan gwaraza da suka tabbatar da dorewar mulkin farar hula a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudurinta na sabunta ginin Nijeriya mafi nagarta da wadata, da kuma haɗin kan kowane sashe na al’umma.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wani taron manema labarai a Abuja, wanda aka shirya domin bitar muhimman batutuwa da suka shafi bikin zagayowar Ranar Demokradiyya ta shekarar 2026.

Ministan ya bayyana cewa bikin na bana yana da muhimmanci, domin ya zo daidai da cikar shekaru uku ƙarƙashin tsarin raya Al’umma na (Renewed Hope) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Wannan bikin ya ba mu damar duba irin ci gaban da muka samu a matsayinmu na ƙasa, da yin bitar tasirin sauye-sauyen da ake yi ya samar, da kuma jaddada ƙudurinmu na gina Nijeriyar da ake fata,” in ji Idris.

Mohammed Idris ya jinjina wa juriyar gishiƙan demokradiyyar ƙasar irin su marigayi Bashorun Moshood Kashimawo Olawale (M.K.O.) Abiola, da sauran magabatan da suka taka rawa da sadaukarwa wajen kafawa da tabbatar da tsarin mulkin demokradiyya a ƙasar.

Ministan ya kuma nuna jajircewar da Shugaba Tinubu ya taka a lokacin gwagwarmayar dawowar ƙasar tsarin mulkin farar hula.

Idris ya bayyana shekaru 27 na mulkin demokradiyya ba tare da katsewa ba a Nijeriya a matsayin wani tarihi da ke nuna jajircewar al’ummar ƙasar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, na ɗayan waɗanda suka halarci taron a matsayin wakilin Shugaban Ƙasa, inda ya taɓo batun mawuyacin halin da tattalin arziki ke fuskanta a yanzu.

Akume ya bayyana cewa matakan cire tallafin man fetur da gyaran ɓangaren musayar kuɗaɗen waje matakai ne masu tsauri amma ɗaukar su ya zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewa.

A cewar sa, sauye-sauyen sun samar da kuɗaɗen shiga da gwamnati ke amfani da su yanzu a fannonin zuba jari domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, aiwatar da manyan ayyuka, da inganta fannin ilimi da lafiya.

Taron na bana dai na zuwa ne a daidai wani lokaci da Al’ummar Najeriya ke cikin matsanancin yanayin rashin tsaro da na rayuwa, matakan da gwamnati ke cewa tana iya bakin kokarin ta, domin shawo kan matsalolin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *