Wani mummunan hari da ake zargin ‘yan ta’adda ne  suka kai ya yi sanadin mutuwar wani hafsan soji da sojoji shida a yankin Rigachikun da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna

Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne ranar Litinin yayin da dakarun sojin suke kan hanyarsu ta dawowa daga wani samame da suka kai domin fatattakar ‘yan ta’adda daga maboyarsu

Kafin harin, sojojin sun yi nasarar dakile ayyukan ‘yan ta’addar tare da kashe wasu daga cikinsu a yayin farmakin da suka kai.

Sai dai yayin da suke dawowa daga aikin ne maharan suka shirya musu kwanton bauna, lamarin da ya janyo mummunar musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

A yayin arangamar ne sojojin bakwai suka rasa rayukansu, yayin da rahotanni suka nuna cewa wasu daga cikin ‘yan ta’addar ma sun mutu sakamakon martanin da dakarun suka mayar.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da manyan ayyukan soji a hanyar Zariya zuwa Kaduna da kewaye domin lalata sansanonin ‘yan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan yawan wadanda suka jikkata ko karin matakan da za a dauka bayan harin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *