Babban Taron APC na Kasa a Abuja ya zo ƙarshe, musamman kan yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar.
Abu mafi ɗaukar hankali shi ne yadda dukkanin mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) suka koma kan kujerunsu ba tare da hamayya ba, ta hanyar abin da ake kira “consensus” ko yarjejeniya.
Me ya sa APC take ganin “Ba Hamayya” ce mafita?
A fili yake lissafin jam’iyyar APC na 2027 ya ginu ne a kan haɗin kai.
Shugabannin jam’iyyar na ganin cewa idan aka bar hamayya ta shigo cikin gida a yanzu, za ta haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobinta, wanda hakan zai ba ɓangaren hamayya damar kifar da gwamnati.
Komawar tsofaffin shugabannin da wa’adin jagorancinsu ya ƙare ko kuma tazarcen Nentawe Yilwatda, alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar na son dorewar tubali a kan tsohon tsarin da aka gino a kai.
Wata babbar dabara da APC ta yi game da batun shugabanci shi ne kauce wa fuskantar sababbin rikice-rikice.
Domin zai yi wahala a gudanar da irin wannan taro ba tare da ya zame wa buƙatar wani bangare tsaiko ba, kamar yadda ya faru a jam’iyyar hamayya ta PDP da yanzu take tafiya a ƙarƙashin shugabanci biyu
APC na ganin barin tsofaffin hannu zai tabbatar da dorewar dabarun shiga da kuma ɗinke ɓarakar zaɓe cikin sauri da sauƙi
Har ila yau tsarin yarjejeniya (ko consensus) yana rage raɗaɗin zuciya da korafe-korafe bayan zaɓe.
To amma inda gizo ke saƙar shi ne duk da yawan gwamnoni da jam iyyar ke da shi, me ya sa take nuna fargaba ko shakku a kakar zaɓen ta bana?
A ka’ida, jam’iyyar da ke da gwamnoni sama da ashirin ciki har da na jihohin Kano da Legas, jihohi biyu da suka fi yawan ƙuri’u, kamata ya yi ta kasance cikin natsuwa.
Tattalin arziƙi da rashin tsaro na daga cikin dalilai da ke hana jam’iyyar mai milki walwala.
A jawabansa na baya-bayan nan Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ce ko rintsawa ba ya iya yi, sakamakon matsalar tsaro da ta addabi yankunan ƙasar.
Matsala ta biyu kuwa ita ce ta taɓarɓarewar tattalin arziƙin jama’ar da ake mulka.
Jam’iyyar na sane da cewa halin matsin rayuwa da tsadar abinci na iya shafar yadda talakawa za su jefa kuri’a.
Don haka ana bukatar shugabanci mai ƙarfi da zai iya tallata manufofin “Renewed Hope” yadda ya kamata.
A baya-bayan nan barazanar haɗakar ɓangaren hamayya ya sake ta’azzara lamurra ga jam’iyar. ‘Ƴan adawa na kai wa juna ziyara daga Kudu zuwa Arewa, a ƙoƙarin haɗe kai domin tunkarar kakar zaɓe da ke tafe.
Masharhanta na ganin APC ta gane cewa ko da tana da gwamnoni, idan gidanta ya rabu, nasara za ta iya kuɓuce mata.
Duk da cewa yawancin gwamnoni suna da tasiri sosai a jihohinsu, rashin samun matsaya guda tsakanin su da sakatariyar jam’iyya na iya haifar da “anti-party” (cin amanar jam’iyya) kamar yadda aka gani a wasu jihohin a 2023.
Tasirin Yilwata da Kwamitin Gudanarwa
Ƙarshe dai mayar da mambobin NWC da kuma tabbatar da Yilwatda na nuna cewa APC ta gwammace ta zauna da tsofaffin fuskokin da ta sani, a kan ta fuskanci sabon ƙalubale.
Tsarin cin zaɓe babu hamayya babban rago ne da jam’iyyar ta yanka don siyawa kanta zaman lafiya.
Sai dai babban kalubalen shi ne: shin wannan sasancin na sama zai iya tasiri har zuwa ga talakan da ke can kauye wanda zai jefa kuri’a a 2027?
Lokaci ne kawai zai bayyana haka.
