Al’umma da dama na shan mamaki da kuma yin tambaya, ko me yasa magoya bayan tawagar Japan ke tsaftace inda suka zauna, yayin kammala wasa? 

Blueprint Radio dake kan mita 105.3 a Birnin Abuja, ta yi nazari kan hakan tare da samun taimakon kirkirarriyar fasaha, inda ta gano cewa al’adar ta fara jan hankalin al’ummar duniya ne a gasar cin kofin duniya da kasar Faransa ta karbi bakunci, a shekarar 1998 — (Gasar Kofin Duniya na farko da Japan ta fara halarta).

Magoya bayan sun ci gaba da nuna wannan al’ada a kowace gasa tun daga lokacin, kuma abin mamaki shine, su kanyi hakan ne ba tare da la’akari da ko sun yi nasara a wasa, ko kuma akasin haka ba.

A shekarar 2018, ‘yan wasan Japan da kan su suka share dakin sauya kaya, bayan an cire su daga gasar, kuma har sukan bar wasikar godiya.

A gasar cin kofin duniya ta bana ta 2026 da ake bugawa a kasashen Amurka, Mexico da kuma Kanada, magoya bayan Japan sun ci gaba da wannan al’ada ta tsabtace filin wasa idan an tashi.

Ko da a wasan da Japan ta buga tare da doke Tunisia da ci 4-0, da wasan da kasar ta buga da Netherlands, inda suka tashi Biyu da Biyu, magoya bayan sun aiwatar da sharar muhallin da suka zauna.

Ga kadan daga dalilan da ya sa magoya bayan ke haka.

Akwai wani karin magana a yaren ‘yan Japan da ke cewa: “Tatsu tori ato wo nigosazu.” — fassara kai tsaye shine “Tsuntsu ba ya barin wani abu a baya.” Ma’anar zancen kuwa itace “Mayar da shi yadda ka tarar da shi.”

A kasar Japan, ana koya wa yara share wurin da suka yi amfani da shi tun daga makarantar firamare, sannan kuma dalibai kan share ajujuwansu, hakan ta sanya ‘yan kasar dabi’antuwa da tsafta.

“A Japan, ana koya mana cewa idan muka yi amfani da wani wuri, ya kamata mu bar shi ya fi yadda muka tarar da shi tsabta, shi yasa muke shara ba tare da malami ya umarce mu ba.” Inji wani magoyin bayan Japan

Dalili na gaba shine, magoya baya na ganin kansu a matsayin baƙi. Sabo da haka, suke ganin hakan a matsayin abin alfahari ne su kawo sauyin da duniya bata sani ba, a matsayin hanyar nuna godiya da girmamawa ga masu masaukin baki.

Har ila yau, ana kiran wannan aikin da yaren Japan “gomi hiroi,” wato “tattara shara,” kuma yana nuna ɗaukar alhakin kulawa ne da wuraren da kowa ke amfani da shi.

Bugu da ƙari, a ranar Jumma’a 19 ga watan Yunin 2026 kwana daya kafin wasan Japan da Tunisiya, Mai Horar da yan wasan Japan, Hajime Moriyasu, ya yi tsokacin cewar “Ina ganin wannan al’ada ce da Japan za ta iya yin alfahari da ita… Na yi imani da yawa daga cikin mutanen mu sun san maganar barin wuri ya fi yadda ka tarar da shi tsabta.”

Kazalika, yawancin magoya bayan da aka yi hira da su kan wannan dabi’a sun jaddada cewa abu ne na yau da kullum, “Wani ɓangare ne na al’adarmu… Muna yin haka don tabbatar da cewa duk abin da muka yi amfani da shi ya kasance mai tsabta domin mutum na gaba ya yi amfani da shi cikin walwala.”

Sai dai wannan dabi’a abace mai wuyar koya musamman ga al’ummar kasashen duniya, da mafi yawanci ke dora alhakin komai kan hukumomi maimakon, tare da zaman jiran dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *