‘Yan Najeriya 67 sun dawo gida daga Afirika ta Kudu, inda suka isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a daren Laraba.
Jirgin kamfanin South African Airways ne ya kawo mutanen, a wani shiri na dawo da ‘yan Najeriya da wasu masu hannu da shuni suka dauki nauyin dawowa dasu.
Kamfanin dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ce wannan shi ne rukuni na biyu na ‘yan Najeriya da kungiyar ta taimaka wajen dawo da su daga Afirika ta Kudu.
Tagomashin da Najeriya ke samu daga cire harajin fiton kaya daga Chaina
A baya, kungiyar ta taimaka wajen dawo da wasu ‘yan Najeriya 83, lamarin da ya sa adadin wadanda aka dawo da su da taimakon kungiyar ya kai 150.
Mista Ikem Ume-Ezeoke da Cif Charles Mba ne suka wakilci kungiyar wajen tarbar wadanda suka dawo, inda suka ba kowannen su tallafin Naira 50,000.
Cif Charles Mba, wanda dan kasuwa ne kuma mai taimakon al’umma, ya bukaci wadanda aka dawo da su, su kasance masu kishin kasa tare da bin dokoki da ka’idojin hukumomin gwamnati.
Ya ce bai kamata abubuwan da suka faru da su a Afirika ta Kudu su hana su sake gina rayuwar su a Najeriya ba.
Mba ya ce akwai fata a gare su, musamman yara da ke cikin wadanda suka dawo, yana mai cewa kalubalen da suka fuskanta ba zai hana su samun ci gaba ba.
Mai kula da kungiyar, Ikem Ume-Ezeoke, ya yaba da kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi a baya wajen taimaka wa ‘yan Najeriya, tare da cewa Najeriya na da damarmaki da wadanda suka dawo za su iya amfani da su wajen gina rayuwarsu.