Babban lauya Femi Falana ya bayyana matsayar sa kan taron kungiyar lauyoyi ta kasa karo na 66, inda yake cewa bai goyi bayan gayyatar da kungiyar tayi wa mutane irin VeryDarkMan da wasu yan siyasa ba.
Cikin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Falana yayi tsokaci kan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan bayyanar matashin da yayi shura a dandalin sada zumunta VeryDarkMan, a taron Shekara da kungiyar ta gudanar a Fatakwal babban birnin jihar Ribas.
jawaban da wadansu malaman mu kamar marigayi Dr. Akinola Aguda ya yi mana a shekarar 1985, ko marigayi Mai Shari’a Oputa ya yi mana a taron shekarar 1987, sun kasance abin tattaunawa a tsakanin al’umma
Babban lauyan ya bayyana matsayin sa cewa kamata yayi masu jawabi da aka gayyata su kasance suna da ƙwarewar aiki a kan batun da ake tattaunawa a kai, domin taro ne na musayar basira da ilimi, bawai nishaɗi ba.
“kungiyar NBA na gayyatar mutanen da suka kafa tarihi, domin gabatar da gagarumar lacca kan ilimi da zai amfani lauyoyi da masu son koyo daga gare su, bawai nishaɗi ba.” Inji Falana
Ya ce zaɓin masu jawabi ya dogara ne kan batun da ake tattaunawa, musamman idan ana magana kan abubuwan da suka shafi harkar tsaron ƙasa.
“Saboda haka, idan za ku kawo ƙwararre domin tattaunawa kan tsaron, daga ɓangaren masu zaman kansu ko gwamnati, dole ne ya kasance ya taka rawar gani a tsarin tsaron ƙasa musamman a halin da take ciki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gayyatar mutanen da ba su da ƙwarewa a kan fannin da ake tattaunawa a kai na iya lalata manufar gudanar da taron.
Martanin sa, ya biyo bayan tambayar da mai gabatar da shirin ya yi masa game da ra’ayin wasu lauyoyi, irin su Farfesa Chidi Odinkalu, wanda ya kare gayyatar VDM a matsayin wata dama ga harkar shari’a domin samun ra’ayoyi daga sauran al’umma waɗanda ke mu’amalar su da tsarin shari’a.
Sai dai Falana ya amsa tambayar da cewa matsayar Odinkalu ta shafi harkar mu’amalar al’umma ne baki ɗaya, kuma hakan bai bayar da damar gayyatar mai jawabi da ba shi da ƙwarewa akan fannin da ake tattaunawa ba.
Falana ya bayyana cewa ya kamata NBA ta koma tsarin gargajiya na gudanar da taron ta, ta hanyar fadada hanyoyin samun ilimi, bisa la’akari da jawaban da wasu fitattun masana shari’a suka bayar a baya, jawaban da suka haifar da muhawara mai ƙarfi a tsakanin al’umma har bayan kammala taron.
“A wancan lokacin, jawaban da wadansu malaman mu kamar marigayi Dr. Akinola Aguda ya yi mana a shekarar 1985, ko marigayi Mai Shari’a Oputa ya yi mana a taron shekarar 1987, sun kasance abin tattaunawa a tsakanin al’umma,” in ji shi.
Falana ya kuma bayyana cewa ya kamata NBA ta riƙa yin aiki da hankali wajen lura da cancantar shugabannin siyasa da take gayyata domin yin jawabi kan tsarin dimokradiyya da dokoki, a ganin sa ya kamata a duba tarihin abinda suka yi lokacin da suke kan mulki.
Musayar yawun ta biyo bayan bayyanar VeryDarkMan ne a wajen taron kungiyar, inda yayi zargin cewar jami’an ‘yan sanda na bayar da bayanan sirri ga masu garkuwa da mutane, kalaman da rundunar ta gayyace shi domin karewa. Sai dai daga bisani yace sai dai su kai shi kotu akai.