Mai fafutukar kafafen sada zumunta Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya ce ba zai miƙa wa ‘yan sanda hujjojin da yake ikirarin cewa wasu jami’an tsaro na taimaka wa masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ba.
Otse ya ce a shirye yake ya amsa gayyatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi masa, amma ya fi son gabatar da hujjojin nasa a gaban kotu, inda ya ƙalubalanci rundunar da ta gurfanar da shi idan tana ganin hakan shine dai-dai, yana mai cewa lauyoyinsa a shirye suke.
A baya ne ‘yan sanda suka gayyaci Otse domin ya gabatar da hujjar zargin cewa wasu jami’an da ke tsaron shingayen bincike a manyan tituna kan gano matafiya masu hannu da shuni, sannan su miƙa bayanansu ga masu garkuwa da mutane domin a sace su.
Rundunar ta ce zargin na da matuƙar muhimmanci, amma ba shi da hujjar da ta gamsar da ita kuma yana iya bata mata suna.
Mu hadu a kotu, a can ne za a gabatar da hujjojin,
VeryDarkMan ya ci gaba da zargin cewa wasu hukumomin tsaro, ciki har da ‘yan sanda, sojoji, jami’an shige da fice da kwastam, suna da hannu wajen taimakawa matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ake cigaba da samun ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane duk da dimbin kuɗaɗen da gwamnati ke warewa domin yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce yana alfahari da kalaman da ya yi, kuma zai ci gaba da yin magana kan abubuwan da suka shafi ƙasa, duk da haka, Otse ya amince cewa jami’an ‘yan sanda na fuskantar matsalar rashin kyayyakin aiki, yana mai cewa gwamnati na buƙatar inganta jin daɗin jami’an domin ƙarfafa tsaron ƙasa.
Kalaman na baya-bayan nan sun zo ne makonni kaɗan bayan da Otse ya zargi mataimakin ‘Yan Sanda da cin hanci dangane da binciken wani lamari da ya shafi ɗan kasuwa Ahmed Tajudeen Akanbi.
Rundunar ta tabbatar da cewa an gayyaci mataimakin ‘Yan Sanda domin yi masa tambayoyi a wani bincike na cikin gida, sannan ita ma ta gayyaci Otse ya gabatar da hujjojin zarge-zargensa.
Rundunar ‘yan sandan ta ce batun laifin da ake magana a kai ya riga ya shiga gaban kotu bayan samun shawara daga bangaren masu gabatar da ƙara.
Yanzu haka VeryDarkMan ya ce a shirye yake ya fuskanci ‘yan sanda a gaban kotu, inda ya jaddada cewa idan suka gurfanar da shi, zai gabatar da hujjojinsa a can. “Mu hadu a kotu, a can ne za a gabatar da hujjojin,” in ji shi.