Hare-haren da aka kai a yankin ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja sun sake jawo kira ga gwamnatin Najeriya da ta ƙara kaimi wajen yaƙi da ta’addanci.
Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bukaci ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen ayyukan ‘yan ta’adda, yayin da gwamnatin jihar ta ce tana da kwarin gwiwar ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.
Majalisar, ta ce hare-haren da aka kai a Gbeji, Kpenya, Giyan Gbasu da Dekara ranar 21 ga Agusta sun yi sanadin mutuwar wasu fararen hula, tare da jikkata da kuma yin garkuwa da wasu.
Ta ce abin da ya faru a Dekara ya fi tayar da hankali, inda ‘yan ta’addan suka shiga babban masallacin yankin yayin sallar Juma’a tare da yin garkuwa da sama da mutum 60, yayin da rahotanni suka ce an kashe kusan mutum 30.
NSCIA ta ce hare-haren sun nuna akwai gibi a tsarin tsaron Najeriya, duk da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a baya.
Ta tuna da aikin ceto na ranar 5 ga Agusta, inda jami’an tsaro suka kubutar da mutum 308 daga dajin Kainji Lake National Park, ciki har da mutum 163 daga Woro a jihar Kwara da 145 daga wasu al’ummomin Borgu.
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta daina dogaro da ayyukan ceto na lokaci-lokaci, maimakon haka ta samar da tsarin tsaro na dindindin wanda zai dogara da bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma.
Ta kuma nemi a sake duba tsarin tsaro a Neja da Kwara da yankunan da ke kan iyakokinsu, tare da ƙara sa ido ta sama da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da gargadin al’umma tun kafin hare-hare.
- Shugaban ƙasa ya bayar da umarnin ceto mutanen da aka sace a Jihar Neja
- Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya ce haɗin gwiwa da Saudiyya zai inganta harkokin tsaro
A nata ɓangaren, Ƙungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da hare-haren, musamman sace dimbin masu ibada a masallacin Kpenya.
Sanatocin sun bukaci jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda aka yi garkuwar tare da ganin an sako mutanen cikin aminci.
Sun kuma nuna damuwa kan rahotannin cewa ‘yan ta’addan sun dasa nakiyoyi a wasu wuraren tare da yin amfani da mutanen da suka sace a matsayin abin ciniki.
A yayin da ake ci gaba da neman waɗanda aka yi garkuwa da su, an kuma kashe hakimin ƙauyen Galla, Alhaji Ahmed Yusuf, tare da wasu mutane huɗu a fadarsa.
Wasu mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne saboda marigayin ya taɓa gargadin su da su daina kai hare-hare a yankin.
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tabbatar da kisan, yana mai cewa an nuna ƙarfin hali da rashin tsoron hukuma wajen kai harin a fadar shugaban al’umma.
Gwamna Bago ya bukaci jami’an tsaro su kamo waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Yayin da Kwamishinan tsaro na jihar, Maurice Justin Magaji, ya ce umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ceto mutanen da aka yi garkuwa da su zai ƙara wa jami’an tsaro ƙarfin gwiwa.
Ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta samar da tallafin kayan aiki gwargwadon ƙarfinta domin ganin an ceto duk waɗanda ke hannun ‘yan bindigar.