Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin “manyan ginshiƙai” waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, domin taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanar da bikin ta a sassan nahiyar Africa ta yamma.

Shugaban ƙasar ya ce harshen Hausa ya bunƙasa sosai, inda ya zama ɗaya daga cikin manyan harsunan haɗin kai da kasuwanci a faɗin duniya.

Ya ce: “Al’ummar Hausawa manyan ginshiƙai ne waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta.

“Ina taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murnar wannan rana ta Hausa, wadda ake bikin ta a fadar Daura mai tarihi a yau,” in ji shi.

Ranar Hausa, wadda ake kuma kira Ranar Hausa ta Duniya (World Hausa Day) ko Ranar Hausa, ana bikin ta ne a kowace shekara a ranar 26 ga watan Agusta.

An fara bikin ne a matsayin wani shiri na kafafen sada zumunta da wani ɗan jaridar Abdulbaki Aliyu Jari ya ƙaddamar, da nufin inganta amfani da harshen Hausa a intanet tare da wayar da kan jama’a game da muhimmancinsa al’adar hausawa.

Tun daga lokacin, bikin ya yaɗu zuwa ƙasashe daban-daban a Afirka, Turai, Gabas ta Tsakiya, Asiya da Amurka, duk da cewa har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta amince da shi a hukumance a matsayin wata rana ta duniya ba.

Hausa na daga cikin manyan harsunan da ake magana da su a Najeriya.

Haka kuma, yana daga cikin harsunan da aka fi amfani da su a Afirka, kuma yana cikin manyan harsunan duniya idan aka yi la’akari da yawan masu magana da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *