Wasu sabbin alkaluma na nuni da cewa adadin guraben aikin yi ga masu shaidar digiri ya ragu zuwa kaso 50 cikin dari a shekarar da ta gabata, yayin da ma’aikata ke kara adadin guraben ayyuka ga wadanda ke da ilmin amfani da fasahar AI.
Dandalin tallata ayyukan yi na Adzuna, ya ce yana da guraben ayyukan masu digiri guda 8,383 a watan Yuli, adadin da ya ragu daga 15,397 a daidai wannan lokacin a shekarar da ta gabata.
Adzuna, ya kuma gano cewa gogayya tsakanin masu neman aiki a dukkan matakai na karuwa, da maki 2 a kowane gurbin aiki guda a watan Yuli, adadin ya karu daga maki 1.93 a shekarar da ta gabata.
To sai dai kuma, wasu sun bayyana cewa waɗannan bayanai na iya kasancewa ba su nuna ainihin halin da kasuwar ayyukan masu shaidar digiri ke ciki, kuma suna iya nuni da sauye-sauye a hanyoyi da ake tallata ayyukan.
‘Yan kasuwa sun bayyana cewa karin inshorar ma’aikata, da mafi karancin albashi na kara tsadar daukar kanana ma’aikata.
Adadin guraben ayyukan yi ga masu shaidar digiri da aka tallata ya kai matsayi mafi ƙaranci tun lokacin da Shafin na Adzuna ya fara adana irin waɗannan bayanai a shekarar 2016.
Dandalin, ya nuna cewa an samu kololuwar neman masu shaidar digiri a shekarar 2017, lokacin da aka tallata fiye da ayyuka sama da dubu 55 a shafinta, wanda ya ninka adadin ayyukan da aka tallata a shafin a watan Yuli fiye da sau shida.
Charlie Ball, kwararre ne kan harkokin koyarwa da samar da ayyukan yi, ya ce alkaluman ba su yi munin da ake tunani ba.
Ya ce alkaluman na iya nuna cewa kamfanoni ne kawai ke rage tallata ayyuka na musamman ga masu digiri, ko da kuwa ayyukan suna nan kuma masu digiri ne ake bukata.
Bisa gogewar sa a wannan bangare, Ball ya ce kasuwar ayyukan masu digiri tana nan, amma tana da rauni dake alamta wani yanayi dake bukatar nazari
Alkaluma a hukumance sun nuna cewa ma’aunin rashin aikin yi tsakanin matasa a Birtaniya, wanda ya haɗa da matasa ‘yan shekara 16 zuwa 24, ya kasance maki 16.2 cikin dari a cikin watanni ukun farko na shekarar 2026.
Adadin matasan da ba sa makaranta, kuma ba sa aiki, ko kuma ba sa karɓar horo yanzu haka ya wuce miliyan ɗaya.
Matasa sun shaida wa BBC a baya cewa sun mika buƙatar neman aiki cikin ɗari-ɗari kafin su sami ko da amsa mai gamsar wa.
Kuma sun nuna takaicin yadda ma’aikatu ke amfani da fasahar AI wajen tace takardun bayanan masu neman aikin.
Bayanai daga Adzuna sun kuma nuna cewa guraben ayyuka a ɓangarorin sufuri, koyarwa, da gini sun karu a makonnin baya bayan nan.
Amma ɓangarori kamar kiwon lafiya, jiyya, karɓar baƙi, da sufurin motocin daukar kaya, na nuna bukatar samun ma’aikata da zasu cike gibin da ake dashi.