Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya sanya sabon kwantiragi da zai ci gaba da zama a matsayin kocin ƙungiyar har zuwa Yuni 2030.
Arsenal ta tabbatar da hakan a hukumance, inda ta ce manyan jami’an da ke aiki tare da Arteta a bangaren horaswa su ma za su ci gaba da kasancewa a ƙungiyar.
- NLC ta fara yajin aikin sai baba ta gani a Abuja kan rikicin malamai
- Radda zai ƙaddamar da ayyuka da shirin tallafa wa al’umma a Matazu
Arteta, wanda ya karɓi ragamar Arsenal a 2019, ya jagoranci ƙungiyar wajen lashe Premier League a kakar 2025/26, bayan Arsenal ta shafe shekaru 22 ba tare da lashe gasar ba.
Ya kuma lashe FA Cup a kakarsa ta farko.
Sabon kwantiragin zai ba Arteta damar ci gaba da gina ƙungiyar da kuma jagorantar ta wajen neman ƙarin manyan kofuna a gida da Turai.