Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, zai ƙaddamar da wasu ayyukan raya al’umma tare da kaddamar da shirin tallafa wa mata, matasa da dattawa a ƙaramar hukumar Matazu.
Daga cikin ayyukan akwai Matazu Semi-Urban Water Scheme, da Cibiyar Koyar da Sana’o’in Haj. Zulaihat Dikko Radda, da ofishin Hisbah na ƙaramar hukumar da kuma motocin sufuri guda biyu da aka samar domin taimaka wa harkokin sufuri da samar da kuɗaɗen shiga.
- 2027: Donald Duke ya ce zai rage farashin fetur zuwa N300 kan lita
- Tinubu ya karrama marigayi Ralph Obioha kan gudunmawarsa ga dimokraɗiyya
- Yabon Bala Mohammed ga Tinubu ya haifar da cece-kuce kan takarar Makinde
Haka kuma, za a gudanar da bikin aza harsashin ginin Asibitin Mata da Yara na Matazu, wanda Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed, Dujiman Katsina kuma ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Musawa/Matazu, ya dauki nauyin sa.
A ɓangaren tallafin, ƙaramar hukumar Matazu za ta bai wa mata 500, da matasa 250 da dattawa 250 tallafin kuɗi, yayin da Dujiman Katsina zai bai wa ƙungiyoyin matasa tallafin naira miliyan uku.
Za kuma a raba babura 100 ga limamai, matasa da masu harkar kafafen sada zumunta, yayin da ƙaramar hukumar za ta raba wayoyin hannu guda 30 ga masu amfani da kafafen sada zumunta.
Gwagware Foundation kuma za ta tallafa wa masu kula da marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi a madadin Uwargidan Gwamnan Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda.